(العدد والإحداد في الشريعة الإسلامية)
ALIYU MUHAMMAD
Domin bayanin waxannan; wato: "iddah" da takaba zai kyautu mu dubi mas'aloli da dama, kamar haka:
Mas'alar farko: Bayani akan "iddah" da dalilai da suka shar'anta ta, da kuma hikimar yinta:
1- "Iddah" a harshen larabci suna ne na "masdari" daga Kalmar "adda, ya'uddu, addan" wanda aka ciro shi daga "adadi da qididdiga"; saboda "iddah" ta qunshi: adadi qididdigagge na: jini ko tsarki, da na watanni.
A shari'ar Musulunci kuma "iddah": suna ne na wani lokaci aiyananne da mace za ta zauna a cikinsa; da nufin bauta ma Allah mabuwayi da xaukaka, ko don alhinin rasuwar miji, ko don ta tabbatar cewa ba komai a mahaifarta.
"Iddah" tana kasancewa ne bayan rasuwa ko shika, kuma don su.
2- Dalilai da suka shar'anta yin "iddah": Dalilan da suka wajabta yin "iddah" sun zo ne a cikin alqur'ani da sunna, da kuma "ijma'i";
Amma daga alqur'ani; to akwai faxin Allah maxaukakin sarki:
ﭽ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭼ البقرة: ٢٢٨
Ma'ana: (Matan da aka riga aka sake su na zaunar da kansu na tsawon tsarki uku) [Baqarah: 228]. Da kuma saboda faxinsa:
ﭽ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨﯩ ﯪ ﯫ
ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﭼ الطلاق: ٤
Ma'ana: (Waxanda suka xebe tsammani daga haila daga cikin matanku, iddansu wata uku ne, haka suma yara mata da basu fara haila ba. Su kuma ma'abota ciki lokacinsu na idda shine su sauke cikinsu) [Xalaq: 4]. Da kuma saboda faxin Allah maxaukakin sarki:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭼ البقرة: ٢٣٤
Ma'ana: (Waxanda suke rasuwa daga cikinku, sai su bar mata; zasu zauna –a matsayin takaba- na watanni huxu da kwana goma) [Baqarah: 234].
Amma dalilin "iddah" daga sunna kuma: Shine hadisin Almiswar xan Makhramah -t- cewa:
"أَنَّ سُبَيْعَةَ الأَسْلَمِيَّةَ –رضي الله عنها- نُفِسَتْ بَعْدَ وَفَاةِ زَوْجِهَا بِـلَيَالٍ ، فَجَاءَتِ النَّبِيَّ r ،
فَاسْتَأْذَنَتْهُ أَنْ تَنْكِحَ، فَأَذِنَ لَهَا فَنَكَحَتْ"([1]).
Ma'ana: (Lallai Subai'ah al-aslamiyyah –t- ta haifu bayan rasuwar mijinta da 'yan kwanaki, sai ta zo wajen annabi –r- tana neman izininsa kan ta yi aure, sai ya yi mata izini, sai ta yi aure). Da wassun waxannan na daga dalilai.
3- Hikimar da ta sanya aka shar'anta "iddah": Hikimar hakan itace: Domin tabbatar da cewa babu xa a cikin mahaifar mace; domin kada a samu cakuxar nasaba. Yana kuma daga cikin hikimar: Bada dama ga mijin da yayi shika ya waiwaici kansa idan yayi nadama; wannan kuma idan shikan da ya aiwatar ana iya kome a cikinsa (na xaya da na biyu ne). haka kuma: Lura da haqqin ciki dana jariri; idan har an rabu, ko an mutu an bar mace da ciki.
Mas'ala ta biyu: Nau'ukan "iddah":
Iddodin da mata ke yi sun kasu kashi biyu: (1) Iddan mutuwa (takaba) (2) Iddan rabuwar aure.
Na farko: Iddan mutuwa (takaba): Wannan kuma shine: idda da take wajaba ga matar da mijinta ya rasu ya barta; shi kuma halin wannan matar baya fita daga xayan halaye guda biyu:
- Ko wannan matar ta zama tana da ciki.
- Ko kuma ta zama bata da ciki.
Idan har ta kasance tana da ciki: To iddarta zai qare ne in ta haife abinda ke cikinta; koda kuwa bayan wassu 'yan-dakiqoqi ne daga rasuwar mijinta; wannan kuma saboda faxin Allah maxaukakin sarki:
ﭽﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﭼ الطلاق: ٤
Ma'ana: (Su kuma ma'abota ciki lokacinsu na idda shine su sauke cikinsu) [Xalaq: 4]. Da kuma saboda hadisin Almiswar xan Makhramata -t- cewa:
"أَنَّ سُبَيْعَةَ الأَسْلَمِيَّةَ –رضي الله عنها- نُـفِسَتْ بَعْدَ وَفَاةِ زَوْجِهَا بِلَيَالٍ ، فَجَاءَتِ النَّبِيَّ r ،
فَاسْتَأْذَنَتْهُ أَنْ تَنْكِحَ، فَأَذِنَ لَهَا فَنَكَحَتْ"([2]).
Ma'ana: (Lallai Subai'ah al-aslamiyyah –t- ta haifu bayan rasuwar mijinta da 'yan kwanaki, sai ta zo wajen annabi –r- tana neman izininsa kan ta yi aure, sai yayi mata izini, sai kuma ta yi aure).
Idan kuma ta kasance bata xauke da wani ciki: To iddanta zai kasance ne tsawon watanni huxu da kwanaki goma, lallai matar da mijinta ya mutu ya barta ba ciki dole zata yi wannan takabar; sawa'un ya sadu da ita, ko kuma bai tava saduwa da ita ba.