Amfanin email address
Email address yana da matukar amfani don yanzu a wannan zamanin anci gaba sosai za ka iya tura sakonni daban-daban ta email ga kowa a fadin duniya. Daga cikin amfanin email akwai wadannan;
* Tura hoto; ana amfani da email don tura hotuna ga Wanda ake bukatan turawa, za Ku iya cinkin gida, television, radio da sauran su, Wanda zai saya kila yana nesa, za a iya daukan hoton abun ta waya ko computer sai a turawa mai sayan don ya gani, Idan ya masa za Ku iya cinki ko da ta email din ne.
* Tura hoto mai motsi (Video); ba a tura hoto kadai amfanin email ya tsaya ba har video ana iya turawa tun daga kan fina-finai, comedy da sauran su, kuma abunda zai fi burge ka da lamarin shine ba kamar Bluetooth, zender ko share it yake ba Wanda sai kuna kusa da Wanda zaka turawa kafin ya turu. Ko mutum yana wani gari ne zaka iya tura mishi duk lokacin da ya bude data sakon zai shigo kamar dai WhatsApp ko Facebook.
* Tura sakon rubutu; Haka kuma ta email zaka iya tura sakonnin rubutu zalla, za ka iya hada hoto da rubutu ko kuma ka hada video da rubutu ka turawa Wanda kake bukatan turawa.
* Yin aikin makaranta; a wasu makarantun musamman Inda aka ci gaba malami yana iya bada assignment sai yace a tura masa ta email, bayan an tura masa sakon zai isa gare shi ya maka kuma ya turawa kowa makin daya samu.
Da zaran ka dauko hoto, video ko kayi Rubuta ka tura nan take yake tafiya sai dai Wanda aka turawa bazai gani ba sai ya bude datan shi, yana budewa Idan akwai network mai karfi sakon zai shiga ba tare da bata lokaci ba.
Sai dai abu daya baza ka iya tura sako ta email ba sai kana da email address, haka baza ka iya turawa Wanda baida email address sako ba. Kenan dole ne sai dukan Ku kun bude email kuma kun San email din juna kafin Ku iya turawa junan Ku ko wane irin sako ta email.
Abubuwan daya kamata ka mallaka kafin bude email address.
Kafin bude email address akwai abubuwa wadanda ya kamata ka sani ko ka mallaka, daga cikin su akwai;
* waya misali kamar android da sauran wayoyi masu kama dasu
* Dole sai da data a layin wayar
* shekarun haihuwa
* lamban waya
* Sunan da zaka sawa email, Da sauran su.
Wadannan abubuwa Dana lissafa ana amfani dasu wajen bude email kenan ya zama dole ka mallake su kafin ka fara budewa.
Sai dai ba lallai bane ka samu daman budewa da Sunan da kake so domin ba a iya bude email daya da suna biyu, Idan ka saka sunan email da kake so idan wani ya Riga ya bude dashi zasu fada maka kuma zasu nuna maka sunaye masu kama dashi sai ka zabi daya ko kuma ka sake gwada wani sunan ko ka saka wasu lambobi a gaban sunan.
Yadda ake budewa
Ga bayanin yadda ake bude email address;
1. Da farko za ka shiga nan Bude email address kyauta don bude wa.
2. Zai bude maka wani guri inda za ka sa sunayen ka
3. Zaka rubuta sunan email address din naka a inda kaga an sa @gmail.com.
Misali idan sunan da kake so shine lambunsadarwa, sai ka rubuta lambunsadarwa@gmail.com
Idan akwai mai amfanin da irin Wannan sunan za su fada maka sai ka chanja sunan sau ka saka @gmail.com a gaban sunan.
4. Sai ka saka password na email na ka, ka samu password mai wahala kuma kar kowa yasan password na ka, Sai ka danna next.
5. Za su bukaci lamban wayar ka sai ka rubuta musu.
6. abu na gaba shine rubuta ranar haihuwa da bambance kai na miji ne ko Mace, sai ka danna next.
7. Sai ka karanta dokoki da ka'idojin su idan ka amince sai ka taba I agree, ka yadda da duk abubuwan da suka fada kenan.
Idan baka yadda ba bazai yiwu ka iya bude wa ba kenan idan kana bukata dole sai ka amince da bayanan su.
Wannan shine yadda za a bude email address da zaran ka danna I agree zasu kai ka zuwa kai sai ka saita duk abubuwan daya kamata ka saita.
Idan kabi wadannan matakai cikin kankanin lokaci zaka mallaki email.