Bayan ka hau kan Facebook din na ka sai ka shiga setting na Facebook.
Dagan za kaga inda aka rubuta privacy setting sai ka shiga gurin.
Idan ka shiga sai ka gangara kasa za kaga who can see your contact information sai ka shiga.
Idan ka shiga za kaga lamban waya ko email address kila ta iya kasance wa dukan su.
Sai ka shiga, idan ka shiga zai nuna maka abubuwa guda uku;
Public; yana nufin kowa zai iya ganin bayanan ka
Friends; abokan ka na Facebook ne kadai za su gani
Only me; kai kadai ne zaka gani, abokai da sauran mutane duk baza su iya gani ba, kuma yafi tsaro.
Sai ka zabi only me saboda yafi tsaro ba Wanda zai ga bayanan ka bare yayi kokarin cutar da kai dalilin ganin, wannan shine takaitaccen bayani game da yadda ake boye lambar waya a dandalin sada zumunta na Facebook kuma duk Wanda yake bukatan boyewa cikin sauki zai boye idan yabi wadannan matakai Dana zaiyana su cikin wannan rubutu nawa.
Ya Kamata a lura da wadannan abubuwa guda uku da ma'anar su da kyau don sune kashin bayan wannan darasin da sune za ka iya chanja yadda kake so lamban wayar ka ta kasance a Facebook, nayi bayanin su a sama saboda muhimmancin su nake sake maimaita su.
Wadannan abubuwa guda uku sune; public, friends da only, sai a lura dasu sosai kuma asan wane za a saka kamar yadda na fada tun farko. Sai dai magana ta gaskiya "Public bai da tsaro ko kadan saboda kowa ne zai ga lamban na ka, dama-dama " friends " abokan Kane kawai zasu gani, sai na karshe "only me" wannan kuma kai kadai za kaga lamban ka.
Atakai ce; Boye lamban waya yana da matukar tasiri wajen dakile yunkurin masu tsoratarwa ta hanyar kiran waya da 'yan dandatsa matsu sace account, idan aka boye lamban waya za a fi samun kwanciyar hankali saboda daga cikin kofofin da za a iya cutar da kai account din ka an rufe wannan sai dai kuma a nemi wata hanyar.
Tambayoyi masu muhimmanci da amsoshin su
* akwai wasu abubuwa da ake bukatan boyewa bayan lamban waya?
Eyh akwai email address da ranar haihuwa (Date of birth)
* shin zan iya goge lamban waya na a Facebook?
Eyh za ka iya gogewa.
*Bayan na goge lamban nawa a Facebook, me zan yi?
Abunda za kayi shine, sai ka saka email address maimakon lamban waya.